Da yammacin Yau Juma'a ne 'Yan Kwankwasiyya Reshen Jihar Neja, sun gudanar da Addu'ar Fidda'un Rasuwar, Marigayi Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, Hakimin Madibi, majidadin Kano.
Shugaban Kungiyar Kwankwasiyya Na Jihar Hon. Dr. Danladi Umar Abdulhameed (tambarin kagara) ne ya Jagoranci Zaman Inda Wani Shehin Malami yayi Addu'ar Samun Rahama da Gafara ga Mamacin.
Anyi Addu'ar Samun Nasara ga Dan Mamacin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kan Bukatar sa Na Samun Shugabancin Kasar Nan.
Daga Karshe Anyi Addu'ar Allah Ya Bamu zaman Lafiya a Arewa da kasa Baki Daya.
0 Comments