2023: Kwankwaso ne zabin alummar Nigeria. Lokaci yayi da za'a yaba kyauta a ramawa kura aniyarta.

 2023: Kwankwaso ne zabin alummar Nigeria. Lokaci yayi da za'a yaba kyauta a ramawa kura aniyarta.





Kwankwaso ya cika dan kishin kasa. A zaben 2015, ya tsaya takarar shugaban kasa a jamiyyar APC akayi abun da akayi a lagos akace shine na biyu. Saboda kishin kasa, ya umarci matasa maza da mata da su fita su zabi  Muhammadu Buhari. 


A zaben 2019, ya fito takarar shugaban kasa saboda alumma basu gamsu da kamun ludayin shugaban kasa muhammadu buhari ba. Ya tsaya takara a jamiyyar PDP, akayi abunda akayi a partachourt aka baiwa mai girma wazirin Adamawa takara Alhaji Atiku Abubakar. Saboda kishin kasa da son kawo sauyi nagari, ya fita yayi tsayin daka wajen ganin jamiyyarsa ta PDP tayi nasara amma akayi abun da akayi shugaba muhammadu buhari ya kara nasara.  


Dan haka cikin yarda Allah da ikonshi, shekarar 2023 kuri'ar talakawan Nigeria ta kwankwaso ce dan kuwa ya nuna halin dattako tare da nuna jajircewa wajen jagorancin samar da sauyi nagari a kasar Nigeria.


Na tabbata da yawa daga cikin alumma sun san abubuwan da suka faru na cin amana da tadewa da wasu daga cikin shugabanni suka dunga yiwa kwankwaso a baya saboda kawai kyashi da ganin cewa meyasa shi zai zama ba suba duk da sun san cewa idan aka daura su baki dayansu  bisa maunin sikeli na samar da ci gaba ga alumma, kwankwaso shi kadai sai ya rinjaye su duba da irin tsaruka masu inganci da ya samarwa alumma mussamman ta fanni ilimi , lafiya da sauransu. 


Yanzu lokaci yayi da yakamata kowa ya kawo tunaninshi kusa, a ajiye hassada a gefe a kalli kasa ayiwa juna gata ta hanyar samar da nagartaccen shugabanci. Saboda na tabbata a halin da muka tsinci kanmu a yanzu a Nigeria kowa yaji a jikinshi. Mallam bahaushe yakan ce ita hassada taki ce, kuma karya fure take bata ya'ya. Na tabbbata masu karatu zasu yarda dani idan nace izuwa yanzu kowanne mai hankali ko bazai fada ba yasan cewa kaf fadin kasar Nigeria mussamman Arewa a yanzu, babu wani Shugaba da alumma suka gamsu da tsare tsarensa da salon jagorancinshi ta fanni kawowa alumma ci gaba da fannin gina dan adam mussamman talakawa marasa hakoran cizo sama da Engr Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso. 


Dan haka anan nakeso nayi kira da babbar murya, da ya kamata duk masu son ganin ci gaban Nigeria da gaske, mussamman shuwagabannin mu na Arewa dasu ajiye kyashi a gefe , suzo a hada karfi da karfe a marawa Kwankwaso baya  wajen samarwa Nigeria mafita mai inganci 2023 dan kuwa a yanzu kaf Nigeria babu wani dan Siyasa da yake numfashi da yake da goyon bayan yan dangwale sama dashi duba da nuna gamsuwarsu a bisa ci gaban da ya samar a fannuka daban daban na roman democradiyya a lokaci da yake rike da madafun iko. 



Post a Comment

0 Comments